Azumi Na Rage Ciwon Sukari, Hawan Jini – Sabon Bincike

Wani teburi da aka shirya domin cin abinci

Kwararru a fannin kiwon lafiya, sun dade suna kwadaitar da masu fama da cututtukan da suka shafi zuciya da ciwon sukari (diabetes) da kuma cututtukan da ke kai wa ga shanyewar barin jiki, da su rika kula da abincin da suke ci tare da yin ayyukan motsa jiki domin inganta lafiyarsu.

Amma wani sabon bincike da aka gudanar a Jami’ar California da ke birnin San Diego da kuma Cibiyar Nazarin Halittu ta Salk a Amurka, ya kara jaddada muhimmancin yin azumi a matsayin maslaha.

Wasu sabbin hujjoji da binciken ya gano sun nuna cewa, yin azumi na tsawon wasu sa’o’i, na taimakawa wajen inganta lafiyar masu wadanda ke da hadarin kamuwa da wasu ko dukkan wadannan cututtuka.

Binciken, ya nuna cewa, wasu mutane da aka ware aka takaita masu sa’o’in da za su ci abinci a kullum, sannan aka sa suka azumci sauran sa’o’in kowacce rana, sun ga karin inganci a lafiyarsu.

An dai sa mutanen da aka yi binciken akansu, da su ci abinci tsakanin sa’o’i 10 ko kasa da haka - har na tsawon makonni 12. Sai su yi azumin sauran sa’o’in.

Bayan haka ne kuma aka gano cewa kibarsu ta ragu, musamma ma ta tumbi, sannan hawan jininsu ya sauka kuma yanayin sukarin da ke jikinsu shi ma ya daidaita.