Babban bankin Najeria yace yace yana da issasun kudin tallafawa

Babban bankin Najeriya yace yana da wadataccen kudin cigaba da tallafawa takardar kudin kasar ta Naira, yayin da darajarta ta sunkuyo kasa a wata mummunar rawar da Nairar ta taka a kasuwannin musayar kudade.

Mataimakiyar,gwamnan babban bankin Najeriya, Sarah Alade ne ta furta haka ta wayar tarho a birnin Iko.

Darajar Naira ta fadi kasa zuwa Naira 170 a kan kowace Dalar Amurka daya.

A hada-hadar hannayen jari da aka gudanar a karshen mako a birnin Iko,hannayen jari sun fadi da kimanin kashi biyar cikin dari.

A watan da ya shige babban bankin Amurka ya fara sayarda takardun basussuka na kasashe masu tasowa da ya saya lokacin koma bayan tattalin arziki.Dalilin haka ya sa alkaluman hannayen jari a Najeriya suka fadi da kimanin kashi 6 cikin 100 a wannan shekarar.