Babu Aikin Da Zai Gagari Mata Idan Aka Basu Dama

Sakina Mahmoud Abdulsalaam

Sakina Mahmoud Abdulsalaam, matashiya mai aiki a banki ta ce tana jin dadin aikinta kuma bata fuskantar wata matsala kamar yadda mata ma’aikatan banki ke cewa.

Ta ce ta fara aiki a banki ne bayan ta kammala karatunta na diploma, a bangaren aiki ne aka tura ta wani banki domin koyon makamar aiki da dalibai ke yi wato IT project- inda bayan kammala wannan horo ne aka bata gurbin aiki har ta fara a wannan banki.

Sakina ta ce da ta dan yi shekaru tana aikin ne ta yanke shawarar komawa karatu inda ta samu gurbin karatu a kasar Benin, domin ta samu takadar degree ko da yake ta fuskanci matsaloli a yayin da take karatun nata.

A cewarta ta yi karatu da aiki ne a tsakanin kasashen biyu wato da nan gida Najeriya da kuma kasar Benin inda aikin ya dinga cin karo da karatun amma duk da haka bata yi kasa a gwiwa ba.

Daga karshe ta kara da cewa ta tsara yadda aikin ta na gida ta yadda bazai taba shafar aikin ta na banki ba, kuma tana jin dadin abinda ta ke, tare da jan hankalin matasa da su kauracewa shaye-shayen kwayoyi su kuma maida hankali wajen dogaro da kai da kawarda zauna gari banza.