Bangaren Saye Da Sayarwa Na ‘Yan Wasan Kwallon Kafa

Dan wasan gaba na Everton Wayne Rooney, ya fara tattaunawa da mahukuntan kungiyar Kwallon Kafa ta DC United, dake kasar Amurka kan batun komawarsa kulob din da taka leda a bana.

Manchester United, tana dab da kammala sayen dan wasan tsakiya na kungiyar Shakhtar Donestk, mai suna Fred, wanda ta ce tana da karfin guiwar za'a kammala cinikin nan da sati mai zuwa.

Manchester City, zata biya fam miliyan £60 wajan ganin ta cimma dogon burinta na sayen dan wasan gefe na Leicester City, Riyad Mahrez, wanda tun a watan janairu ta ke kokarin ganin ta kawo shi kulob din ta.