Jami’an bankin baiwa kananan ‘yan kasuwa rance, mai suna tattali, Micro Finance, da wasu masu hulda dashi suka yi zargin anyi awon gaba da kudadensu, a jihar Neja, sun yi bayanin matsalar da ta afkawa bankin, da har ya shiga wannan hali.
Daya daga cikin darektocin bankin, Alhaji Muhammadu Kudu, ya shaidawa wakilin muryar Amurka, Mustapha Nasiru Batsari, cewa masu karbar bashi a bankin ne suka nemi durkusar dashi. amma kawo yanzu, an shawo kan wannan matsalar,
Ya kara da cewa matsalar da aka samu a bankin kennan ba wai wani ya sace kudi bane, jami’an bakin ne suka bada rancen kudaden da ya zarce abun da ya kamata.
Babban darektan ma’aikatan dake kula da wadannan kananan bakuna, a jihar Neja, Malam Bako Muhammad Bawa, yace sun yi kokarin shawo kan matsalolin da suka addabi wadannan bankuna, a saboda haka ya shawarcin jama’a, dasu kwantar da hankalinsu.
Your browser doesn’t support HTML5