Bashir Bello Danshila: Sana'ar Girki Ba Ta Mata Ba Ce Kadai

Bashir Bello Danshila

A shirinmu na mata da sana’a wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir, ta samu bakunci daga wani matashi mai suna Bashir Bello Danshila, mai aikin da aka fi sani da mata wato girke-girke.

Ya dauki akalla shekaru goma yana sana’ar girke-girke inda ya ce ya fara ne da wanke-wanke har ya kai ga shi ma ya bude wajen girke-girke .

Da ya ga yana da sha’awa a wannan harka ta girki ne ya sa har sai da ya je ya koyi yadda ake girke-girke, domin ya inganta sana’arsa wanda yana daga cikin mutane na farko, namiji da ya fara koyar da girke-girke.

Ya ce yanzu zai gudanar da wata gasa ta girki wato ‘Tukunyar Gaske’ gasar da ba a taba yin irinta ba a birnin Kano, inda ya ke bukatar wadanda su ka iya girki su fito domin nuna kwazonsu.

Ya ce ga wadanda za su lashe gasar, akwai kyautar fom na koyar da girki da za a basu, kuma yana sa ran nuna wa al’umma cewar sana’ar girki ba ta mata kawai ba ce, maza ma za su iya shiga wannan gasa.

Ya ce Kuku namiji abu ne mai muhimmanci, domin namiji ya koyi yadda ake girki na da matukar muhimmaci ga harkokin rayuwa na yau da kullum.

Ga rahoto a sauti daga wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.

Your browser doesn’t support HTML5

Bashir Bello Danshila: Sanar Girki Bata Mata Bace Kadai