Bayern Munich Da Real Madrid Zasu Kara A Gasar Uefa 2016/2017 (Quarter final)

Bayan kammala wasannin cin kofin zakarun nahiyar turai Uefa da na Europa na shekaraR 2016/2017 a matakin zagaye na Goma sha shida a wannan satin inda a kowane bangare kungiyoyi guda takwas suka samu hayewa zuwa zagaye na gaba Quarter Final.

Yau 17/3/2017, an fidda jaddawalin kungiyoyin da zasu gwabza a tsakaninsu a matakin wasan kusa da na kusa da na karshe Quarter final.

A bangaren Uefa kuma, kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, zata kara da Leicester City, Borussia Monchenglabach, da Monaco, sai Bayern Munich, da Real Madrid.

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus, zasu kece raini da Barcelona, za'a buga wasanninne a ranar Talata 11/4/2017 a karawar farko, karawa ta biyu kuwa za'ayi ta ne a ranar18/4/2017.

A bangaren Europa kuwa ranar Alhamis 13/4/2017

Anderlecht, zata karbi bakuncin Manchester United

Celta Vigo zata kara da Genk sai kuma Ajax su fafata da Schalke 04

Lyonnais su barje gumi da Basiktas

Inda za'a dawo karawa na biyu ranar 20/4/2017