Bincike Ya Nuna Kusan Yara Miliyan 200 Ne A Duniya Da Basa Samun Damar Cimma Burin Su Na Rayuwa

A wani rahoto da wakiliyar muryar Amurka sashen Ingilishi ta gabatar, bincike ya nuna cewa sama da shekaru ashirin da suka gabata an sami raguwar mace macen kananan yara a duniya baki daya, taimakon biliyoyin daloli da sauran muhimman kokarin da sauran kasashen duniya suka yi, ya taimaka wajan ganin an cimma wannan buri na rage mace macen kananan yara a duniya.

A cewar wani kwamitin kwararru, yanzu abin da ya rage shine a hada karfi da karfe domin ganin an taimaka ma wadannan yara cimma burin su na rayuwa.

Sabuwar kasidar da kungiyar masana harkokin zamantakewa da kwararru a fannin kiwon lafiya suka wallafa ta bayyana cewar akwai kusan kananan yara miliyan dari biyu da basa iya cimma burin su na rayuwa a duniya.

Kuma a cewar masanan, rashin cudanya da kuma kulawar wadanda alhakin hakan ya rataya akan su ne musabbabin wannan matsala.

Taron ya kumshi masana 32 daga kasar Amurka, da ma’aikatar harhada magunguna, kuma sun bada tabbacin cewar rashin abinci mai gina jiki na iya shafar lafiyar yara.

Haka ma rashin kwanciyar hankali, da rashin kulawara da danne masu hakki na haifar da rashin ingantuwar kwakwalwar yara.