Habiba Abubakar wata matashiya mai burin koyar da harshen turanci domin inganta harshen turanci a tsakanin matasa ‘yan arewa a cewarta domin shine harshen da Najeriya ke amfani da shi.
Ta ce ta lura da cewar a yankin arewa, harshen turanci yayi karanci hakan ne ya sa da zarar ta kammala karatunta na Turanci abinda ta fi sha’awa shine koyarwa duk kuwa da cewa malamar makaranta na daga cikin sana’ar da matasa basa so a yanzu kuma mafi kaskanci.
Ta kara da cewar kasancewarta malamar makaranta zai bata damar gyara kura-kuran da ake samu na koyar da harshe tare da cusawa dalibai son harshen.
Malama Habiba, ta ce babban abinda ke ci mata tuwo a kwarya bai wuce yadda al’umma ke yi mata kallon mara da’a duba da irin dadewar da take yi da zarar ta tafi makranta inda a mafi yawan lokuta sai dare take dawowa.
Your browser doesn’t support HTML5