Cajin Waya Cikin Dakikoki Sittin

Superstorm Sandy

Takaicin jiran awanni domin cajin wayar hannu zai zamanto wani abune na tarihi, godiya ga sabuwar fasahar batiri da aka kera ta yin amfani da alminiyan wadda za’a iya caja shi cikin dakikoki sittin, abune mafi aminci da kuma kyau ga muhalli, inji masana kimiyya.

Baturan da ake amfani dasu a yanzu haka ana ‘kerasu ta yin amfani da sinadarin alkaline, wanda ke gurbata muhalli, da kuma baturan lithium-ion wanda wayoyin hannu da kananan kamfutoci ke amfani dasu, wadannan batura dai na iya kamawa da wuta cikin gaggawa suna daukar lokaci kafin suyi caji.

‘Daliban jami’ar Standford sun kirkiro sabuwar fasahar yin amfani da alminiyan wajen kera batirin da zai ‘dauki caji cikin gaggawa, ya kuma dade yana aiki zai kuma zama mai rangwamen farashi. Batirin baya jan wuta mai yawa kamar yadda batiran lithium-ion ke yi.

Farfesan kimiyya na jami’ar mai suna Hongjie yace, mun kirkiri wannan fasahar tayin amfani da alminiyan wajen kera batiri, wanda muke zaton zai maye gurbin batirin da muke amfani dashi a duniya, baturan da muke amfani dasu suna gurbata muhalli, idan aka duba batirin lithium-ion har wuta yake kamawa wani lokuta. Batirin mu bai kama da wuta ba komai za’a yi masa.