Chelsea Ba Ta Bukatar Rabuwa Da Samuel Iling-Junior

Wasu manyan kungiyoyin kwallon kafa da dama sun fara nuna sha'awar su akan dan wasan Chelsea, Samuel Iling-Junior, kungiyoyin sun hada da Bayern Munich da Paris Saint-Germain da Ajax da kuma Schalke.

Ita dai Chelsea tana son ta ci gaba da rike dan wasa Iling-Junior, wanda bata son rabuwa da matashin mai shekaru 16 da haihuwa, saboda wasu kananan kudade da za’a bata.

Kwantiragin dan wasan na shirin karewa nan kusa, kuma babu wata kungiya da ta sa hannu kan sabuwar yarjejeniya da shi.

Marcin bulka

PSG da Bayern sun sami nasarori kan sayen 'yan wasa matasa daga Chelsea, yayin da Marcin Bulka da Jamal Musiala dukkanin su suka tafi a yanayi mai kama da juna, su kuwa Schalke da Ajax suma sun tura 'yan wasan su zuwa kwalejin horar da ‘yan wasa da ke Cobham don samun kwarewa ta musamman.