Gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya dan kasar Portugal, mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Cristiano Ronaldo, na fuskantar barazanar dakatarwa a wasanni Goma sha biyu 12 daga hukumar wasannin kasar Spain, a sakamakon rashin da'a da ya nuna a wasan da sukayi da Barcelona na Super Cup, ranar 13/8/2017.
Bayan da alkalin wasa Ricardo De Burgos Bengoetxea ya bashi Jan kati,
Acikin bayanansa, alkalin wasan ya rubuta cewa bayan ya ba Cristiano, Jan kati dan wasan ya bangajeshi, yin hakan ya saba wa doka ta 96 ta dokokin kwallon kafar tarayyan Spain,
Don haka binceke na ci gaba da gudana, kuma idan aka tabbatar da wannan laifi, dan wasan na iya rasa buga wasanni akalla 4 ko 12 na kasar Spain.
Kungiyar ta Real Madrid, dai lallasa abokiyar hamayyarta, Barcelona da ci 3-1 a wasanda da suka buga, wasan ya gudanane a filin wasa na Camp nou.
Real Madrid, ta samu nasarar saka kwallonta ta farko ta kafar mai tsaron baya na Barcelona, G, Pique bayan da ya ci gida (Own Goal) a minti na 50 da fara wasan.
Daga bisani Barcelona, ta rama a mintuna na 77, a bugun (penalty) ta kafar dan wasanta Lionel Messi,
Cristiano Ronaldo ya jefa Kwallo ta biyu a mintuna na 80 sai M. Asensio yajefa ta ukku a na dab da tashi.
Your browser doesn’t support HTML5