Cututtukan Dake Damun Matasa A Yau

ម៉ុត វណ្ណ ជាមួយ​កូនប្រុស ជា​អ្នក​ខេត្តបាត់ដំបង បាន​ឆ្លង​មេរោគ​HIV ពី​ប្តី​របស់​គាត់​ដែល​បាន​ស្លាប់​ទៅ​ហើយ​ដោយសារ​ជំងឺ​អេដស៍។ រូបនេះ​ថត​នៅ​ថ្ងៃ​ទី២១ ខែកញ្ញា ឆ្នាំ២០០៣។Moth Vann sits on a bed cradling her son in Battambang September 21, 2003.Moth Vann lost

Kan batun cututtukan dake damun matasa mata da maza a nahiyar Afirka, wakilan mu da dama sun zanta da matasa daga kasashen Najeriya, Kamaru da Nijar, inda suka tambayi yawancin matasa wacce cuta ce suke ganin tafi addabar matasan mu a wannan zamani?

Shaye shayen miyagun kwayoyi da yawan cututtukan da ake samu wajen yin jima’i, sune manya manyan amsoshi biyu da muka samu a kasashen uku da wakilan mu sukayi wannan tambayar.

Amfani da miyagun kwayoyi ya zama ruwan dare ga matasa a duniya, musammam ma idan muka duba kasashen Hausa, zamu ga matasa sun mai da miyagun kwayoyi a matsayin wani abun nishadi. Wadannan kwayoyi na kawowa matasan mu il’loli da dama a rayuwar su, tabin hankali shine ‘daya daga cikin babbar illa da kwayoyin ke kawowa, rashin yin karatu, sace sace, samun matsalolin lafiyar jiki da sauransu.

Rashin sanin ilimin Jima’i babbar ga mutum har ma ga al’umma baki ‘daya, matasa maza da mata a wannan zamani na yin jima’i batare da sanin muhimmancin kare kai ga kamuwa da munanan cututtuka ba, kadan daga cikin ire-iren cututtukan sun hada da cuta mai karya garkuwar jiki wato ‘kanjamau, ciwon sanyi, tinjere da ‘dan kanoma. Kamuwa da ‘daya daga cikin wadannan cutattuka kuwa na kaiwa ga rashin lafiya mai tsanani harma da yada su ga sauran mutane.

Matasa maza da mata wannan kalubale ne gareku, kare kai ga shiga ire-iren wadannan hali shine zai kare rayuwar ku da lafiyar, kai harma lafiyar masoyan ku dama duniya baki ‘daya.