Daliban Obama YALI a Najeriya Sun Shirya Wayar da Kan Matasa a Kan Siyasa

Shugaban Amurka Barack Obama da YALI, Washington, D.C.

Bisa ga yunkurin kasar Amurka na tallafawa kashashen Afrika, ta bangaren ingantacen shugabanci, kasuwanci da tattalin arzikin kasa. A shekarar da ta gabata shugaban kasar Amurika Barak Obama ya gayyato matasa dari biyar da ga kasashen Afrika wadanda sukazo nan Amurika aka koyar da su a fanoni daban daban a jami'o'in kasar Amurika, da zumar su koma kasashen su, don taimakawa cigaban kasashen.

Bisaga wannan horaswar da wannan matasan suka samu a nan amurika, wasu daga cikin wadannan matasan, kamar Dr. Ashiru Abuabakar Adamu, Barrista Safiya Nuhu, da Fatima Ibrahim, dukkansu sun cigajiyar wannan shirin da akaima dakani da "Mandela Fellowship" sun shiryar da wani taro don wayar da kan matasa dangane da hanyoyin da zasu bi su, taimaka ma cigaban kasar, kuma su ilmantar dasu hanyoyin da zasu bi su gujema bangar siyasa.

A tattaunawar mu da Dr. Ashiru Adamu, yayi muna Karin haske kamar haka, yace sun shiryar da wannan horaswar ta kwana daya da zasu gudanar a dakin taro a tsangayar shari’a na Jami’ar Bayaro da ke birnin Kano, gobe idan Allah ya kaimu da karfe goma na safe. Kuma suna bukatar duk wani matashi ko matashiya da su halarci wannan taron don jin sako daga shugaban kasar Amurika Barak Obama. Kana akwai manya manyan malamai daga bangarori da ban da ban, da kuma addinai kana da ‘yan siyasa da zasu gabatar da kasida a wajen wanan taron. Ya kara da cewar, suna kira ga matasa da kada su bari ayi amfani da su wajen cinma wani buri da zai iya sa kasar cikin halin kakani kayi.

Your browser doesn’t support HTML5

Daliban Shugaba Obama - 3'19"