Dan Hajiya na Nishadantarwa Baya Ga Tallace Tallacen Biki

A shirinmu na nishadi a wannan mako dandali ya samu bakuncin Ghali Ali Abdullah DZ wanda aka fi sani da dan Hajiya mawakin fina finai , tallace tallace dama wakokin biki.

Dan Hajiya ya fara harkar wakokin fim ne a shekara ta 2001 wanda aka fara sa wakarsa ta farko a fim din ‘Ibro dan dauda sannan aka sake sa ta a fim din Kasaita’.

Ko da yake ya ce wakokin guda biyun da ya fara yi ba su ne bakandamiyarsa ba illar wakar tallan fulawa mai kobo ita ce ta sa yayi fi ce.

Dan Hajiya na nishadantarwa ba ya ga tallace tallacen biki , ya ce yana samu basirar hada wakokin fina-finai da ma na tallace tallacensa ta hanyar kallon yara idan suna wasa domin kuwa ta nan ne yake samun hikimar hada waka.

Ya ce burinsa ya bunkasa harshensa na Hausa.

A fannin tsegumi kuwa a ranar litinin din da ta gabata ne aka daura auen jarumi Adam Zango a jamhuriyyar Kamaru.