WASHINGTON, DC —
Wani dan shekaru 94, a kasar Amurka za’a kasance daya daga cikin wadanda suke da yawa shekaru da ya samu digiri daga jami’ar Virgina.
A Wani Sanarwa da jami’ar, Virginia, ta fitar tace Anthony Brutto, ya kwashe shekaru 75, kafi ya kai ga chima burin sa na kamala karatun jami’a.
Anthony Brutto, ya fara karatun jami’a, a shekara 1939, a lokacin da ake biyar dalar Amurka $50, kudin shiga jami’a.
Zuwa yakin Duniya na biyu yasa shi barin makaranta, a shekarar 1942, a shekara 1946 ya kuma amma rashin lafiyar matasa yasa shi janye wa.
Anthony Brutto, yace kamala karatun jami’a ya kasance babban burin sa , a cikin raha ya cewa zai huta kada kafi ya fara karatun digiri na biyu.