An soki dan wasannan me tsaron gida Ronaldo, da rashin cin kwallaye a shekara 2015. Shi dai Cristiano Ronaldo, ya samu nasarar saka kwallaye 5 cikin wasa 1 a karon farko a tarihin wasanshi na kwallo cikin kungiyar Real Madrid, inda aka tashi da ci 9-1 yau lahadi.
Shi dai dan wasan na kasa-da-kasa ya samu damar fara saka kwallayen nashi ne bayan mituna 30 a filin wasan Santiago Bernabeu, inda yayi wani wasa me kyau cikin mituna 8 a farkon wasa, sannan kuma ya saka sauran 2 a tsakanin mintuna 54 zuwa 89.
Shi dai dan wasa Ronaldo ya samu nasar cin kwallaye 4 a wasa daya har sau 3 kenan tun bayan komawarshi klob in Real Madrid daga klob in Manchester United a 2009, na kusa shine na watan Satunbar shekarar da ta gabata.
Amma a baki daya tarihin wasanshi be taba samun nasara irin wannan ba wanda yayi a cikin mintuna 90.