Darajar Kungiyoyin Kwallon Kafa A Matsayin Kudi

Mujallar Fobes, ta fitar da sunan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United a matsayin wadda ta fi kowace kungiyar kwallo daraja duniya, an kuma kiyasta darajarta akan kudi wuri na gugar wuri dalar Amurka Biliyan 4.12, wato tana kan gaba da kungiyar Real Madrid wadda ita kuma darajarta ke daidai da dalar Amurka Biliyan 4.08, a matsayin ta biyu sai kuma Barcelona da ke da dala Biliyan 4.06, a matsayin ta uku.

Ga yadda aka tsara jerin darajar shahararrun kungiyoyin;

  1. Manchester United, Dala Biliyan ($4.12)
  2. Real Madrid, Dala Biliyan ($4.08)
  3. Barcelona Biliyan, Dala ($4.06)
  4. Bayern Munich, Dala Biliyan ($3.06)
  5. Manchester City, Dala Bilyan ($2.47)
  6. Arsenal, Dala Biliyan ($2.23)
  7. Chelsea, Dala Biliyan ($2.06)
  8. Liverpool, Dala Biliyan ($1.94)
  9. Juventus, Dala Biliyan ($1.47)
  10. 10.Tottenham Hotspur, Dala Biliyan ($1.23)