Daya Daga Cikin Mawakan Hip-hop Psquare Ya Bukaci Su Rabu

Psquare

Shahararrun Mawakan Hi-hop din nan na Najeriya, Peter da Paul Okoye, da aka fi sani da Psqure, sun raba-jaha daga matsayin su na tsintsiya madaurin ki daya.

Mujallar Vanguard ta wallafa cewar a wata wasika da Lauyan mawakan Festus Keyemo, ya gabatar, Peter ya bukaci a kawo karshen yarjejeniyar kasancewarsu a matsayin kungiya. A cewar wasu kafafen yada labarai jiya litini, Peter ya yanke wannan shawara ce a sakamakon zargin dan’uwansa Paul, da babban yayansu wanda kuma shine manajan su Mr Jude, cewa Paul ya daina hada kai da shi wajan aiwatar da lamurra, har ma ya soke shirin ziyarar su Amurka.

Mawakin ya kara da cewa dan’uwan nasa Paul, na yada labaran kanzon kurege dangane da matarsa da iyalinsa a shafin yanar gizo, ya kuma kara da cewa iyalinsa sun sami sakonnin barazana iri daban daban daga shafukan yanar gizo.

Peter ya zargi babban yayan su Mr Jude, wanda shine manajansu da yin barazanar hallaka shi, da kuma harbe matar sa Lola, dalili Kenan da yasa Paul ya ga cewa ya kamata su kaim karshen wannan takaddama da taki ci taki cinyewa, dan haka abinda yake bukata kawai shine su rabu daga matsayin kungiya.

An yi ta yada labarin tafiyar da Peter ya yi zuwa jihar Philadelphia ta kasar Amurka shi kadai ba tare da dan’uwansa ba a Shafukan yanar gizo (Snapchat) inda ya rubuta cewa “daga yau sunana Mr P, kun san wani abu? Yanzu haka Ina dab ta hawa fara wasa”. Wannan ya biyo bayan rubutun da dan’uwansa Paul, ya wallafa a shafin Instagram, cewar “mace kadai ke iya zuwa wurin da ake zman lafiya ta nemi ta wargaza shi”.

'Yan'uwan junan sun dukufa wajan yi wa maganganu a kan kafofin sada zumunta na yanar gizo a cikin' yan kwanakin nan, kuma wannan ya tabbatar da jita-jitar cewa akwai matsaloli a cikin dangantakar su.