Dubu Ta Cika Barayin Sun Shiga Hannu

Rundunar ‘yan Sandan Jahar Kano, ta cafke mutane 69, wadanda ‘yan fashi da makami da barayin Shanu ne. a watan da ya gabata, a wani yunkurin na kawar da bata gari a jahar.

Kwamishinan ‘yan Sandan jahar Muhammad Katsina, ne ya bayana haka jiya a lokacin da ya ziyarci Gidan-kare a karamar hukumar Sumaila, a jahar ta Kano, domin tsara yadda za’a kawar da bata gari dga yankin.

Rahotani daga kauyen Gidan- Kare, su nuna cewar jama’a, sun kaura daga garin saboda ‘yan fashi da makami sun addabi jama’ar garin.

Kwamishinan ‘yan Sandan, ya ce 46, daga cikin wadanda aka kama rundunar ta dade tana farautar su domin suna cikin wadan da suka addabin jahar.

Ya kara da cewa an samu Awakai da Tunkiyoyi guda 20, bindigogi 31, da harsasai 240, da kuma Shanu 68, a ciki an maida 30, ga masu Shanun.

Ya ce daga bisani an kama wani takadari shugaban ‘yan fashi mai suna Datti Rodi, wanda rahotani sun nuna cewar yana da kusa mutane 200, a karkashin sa.