Gwamnatin kasar China ta kara ingancin katangar kariya da ake kira firewall a turance, a cigaban da take na kokarin kare da tantance duk wasu bayanai da ka iya shiga kasar ta kan yanar gizo.
Wannan karin inganci na katangar zai baiwa gwamnatin kasar damar tacewa da zabin duk wasu bayanai dake kan duniyar gizo. Wanda wannan lamari ka iya kara kuntatawa rayuwar mutanen China, alokacin da gwamnatin kasar ta haramta yin amfani da yawancin hanyoyin sadarwa da yawancin kasashen duniya ke amfani da su a wannan zamani, kamar su facebook, Twitter, da Google harma da shafin kallon bidiyo na YouTube.
Wadannan hanyoyin sadarwa na kan yanar gizo dai mutane na amfani dasu domin cudanya ko zumunci da mutanen dake wasu kasashe, ana ma yin amfani da hanyoyin wajen gudanar da kasuwanci a kasashen duniya.
Gwamnatin china dai na amfani da ire-iren wadannan damar don ganin tayiwa ‘yan kasar hannunka mai sanda kan abin da gwamnatin China ke so.
Your browser doesn’t support HTML5