Facebook Zai Fara Amfani Da Manhajar Gano Masu Yunkurin Hallaka Kansu

Facebook zai fara amfani da wata manhaja don gano mutanen da ke cikin raunin iya ‘daukar rayukansu, a kuma nema musu taimako.

Wannan hanya ta kare afkuwar ‘kashe kai’ ta kai shekaru 10 da kirkirowa, amma yanzu Facebook na gwajin wata sabuwar hanyar da zata rika gano mutanen da suke da wannan matsala ba tare da bata lokaci ba.

Wasu mutane kanyi kokarin kashe kansu bayan da suka shiga wani hali na damuwa ko kunci, wannan lamari dai yafi kamari ga yara da matasa.

Ita wannan manhajar zata rika lura da abubuwan da masu amfani da dandalin Facebook suka kafe, da zarar ta hangi wasu kalamai dake nuna cewa mutum yana yinsu ne cikin fushi ko damuwa, to zata sanar da mutanen dake kusanci da shi domin a dauki mataki cikin gaggawa.

A cewar Facebook ana samun mutane suna kanshe kansu cikin kowacce dakila 40, haka kuma abin yafi tsamari ga matasa ‘yan shekaru 15 zuwa 29.