Falcons Na Son a Biya Su Daidai Da Super Eagles

Kungiyar Super Falcons Ta Najeriya

Bayan Dumbin nasarorin da kungiyar matan Najeriya ta Super Falcons ta samu, yanzu haka kyaftin din kungiyar ta bukaci a rika biyansu albashi daidai da takwarorinsu maza wat kungiyar Super Eagles.

Kyaftin din kungiyar kwallon kafar mata ta Najeriya Super Falcons, Desire Oparanozie, ta ce kungiyar kwallon kafa ‘yan mata ta Najeriya ta cancanci a rika biyanta kudi daidai da takwarorinsu maza wato Super Eagles.

Kungiyar Super Eagles ita ce akan gaba a cikin kungiyoyin da aka fi biya a nahiyar Afirka kuma tun da nasarorin da kungiyar Super Falcons ta samu ya fi na takwarorinsu maza, ba wai sun kauce hanya ba ne don sun bukaci a biya su kudi daidai, a cewar kyaftin din Super Falcon, Oparanozie.

Oparanozie ta bayyana hakan ne yayin wani taro da aka yi kan irin rawar da mata ke takawa a fagen wasanni, kamar yadda jaridar yanar gizo ta Premium Times ta ruwaito.

Kungiyar Super Falcons a nahiyar Afrika ita ce tafi samun nasarori akan sauran kungiyoyin kasashe da ta lashe kofina tara kuma ta zama ita ce kungiya daya tilo daga Afrika da ta buga wasanni a duka gasar cin kofin kwallon kafar mata ta duniya guda takwas.

Akan biya kungiyar Super Falcons dala 3,000 a wasan da suka yi nasara ko kuma dala 1,500 idan suka tashi kunnen doki a kowacce gasa, yayin da Super Eagles ke karbar dala 10,000 a wasan da suka yi nasara ko kuma dala 5,000 a wasan da suka tashi kunnen doki.