Fernandes Zai Iya Maye Gurbin Pogba - Scholes

Tun bayan ficewar dan wasan tsakiya na kungiyar Red Devils a watan Janairu, masoyan dan wasan suke cike da murna.

Bruno Fernandes ya saje da ‘yan wasan kungiyar Manchester United, duk da cewa dama yana da cancantar da ta dace, a cewar Paul Scholes, wanda yake da tabbacin cewa tafiyar Paul Pogba, ba zai girgiza kungiyar ta Red Devils ba ko kadan.

Paul Pogba

Rade-radi na ci gaba da yawo cewa a lokacin bazara mai zuwa yayin gasar cin kofin duniya, dan wasan tsakiyar zai tafi wata kungiya a matsayin aro.

Real Madrid ta dade tana kaunar Paul Pogba mai shekaru 26 da haihuwa, amma labarin komawarsa Juventus ya fito ne daga bakin wakilin dan wasan, Mino Raiola.