Frank Lampard Ya Dorawa VAR Laifin Rashin Nasararsu

Frank Lampard

Kocin Chelsea, Frank Lampard ya fusata saboda wasu dalilai bayan rashin nasara da kungiyarsa ta yi, inda aka tashi wasa da ci 2-0 wanda Manchester United ta yi nasara, da suka hada da shawarwarin da aka yanke bisa la'akari da sabarun sa ido a gasar kwallon kafa.

Chelsea ta samu damar jefa kwallaye biyu, amma aka yi amfani da fasaha aka hana ta kwallayen, kuma aka ki bada jan kati da zai taimakawa kungiyar kwallon kafar da ake wasa a gidanta.

Hukuncin da aka yanke tare da gudummuwar VAR din bai yima kocin da sauran magoya bayansu dadi ba, wanda hakan yasa Lampard cewar mai yasa ba’a hukunta dan wasa Harry Maguire ba, bisa dalilin harbin dan wasa Michy Batshuayi da ya yi.