Ga Jaddawalin Wasannin Kihuwa Daya (Knockout) Rasha 2018

A jaddawalin zagaye na kasashe goma sha shida da zasu fafata a gasar cin kofin kwallon Kafa na duniya na bana wanda yake gudana a Rasha, a matakin kihuwa daya (Knockout) wanda za'a fara ranar asabar 30/6/2018

Ga jerin wasannin kamar haka.

A ranar asabar kasar France da Argentina,

Uruguay, da Portugal,

Ranar Lahadi 1/7/2018

Spain zata kara da Mai masaukin baki kasar Russia, sai Croatia da Denmark,

Ranar Litinin 2/7/2018

Brazil, da kasar Mexico, kasar Belgium, da Japan,

Ranar Talata 3/7/2018

Kasar Sweden da Switzerland sai kuma kasar Colombia da kasar England,

Wadannan sune kasashe goma sha shida da zasu kara a tsakaninsu.

Bayan kammala wasan zagaye na uku a matakin rukuni, ga yawan jimillar kwallaye da Kati da aka bayar a cikin wasanni 37 da aka buga cikin kwanaki goma sha biyar, an bada Katin gargadi (Yellow Card) guda 163 sai kuma Jan kati (Red Card) 3.

An zurara kwallaye 122, a raga, an kuma samu bugun daga kai sai mai tsaron gida (Penalties) 25 an samu nasarar jefa guda 19 an baras da 6, an samu kwallaye 9 wadanda aka sha gida wato (Own Goals) akwai kuma kwallaye biyu da aka haramta su wadanda suke kan gaba wajan zurara kwallon sune kamar haka.

Harry Kane na kasar (England) mai kwallaye 5 sai Romelu Lukaka (Belgium) kwallo 4 Cristiano Ronaldo (Portugal) 4 sai kuma Denis Cheryshev daga (Russia) 3, akwai Diego Costa na (Spain) mai kwallaye 3.

Your browser doesn’t support HTML5

Ga Jaddawalin Wasan Kihuwa Daya (Knockout) Rasha 2018