Gareth Bale Na Tare Da Madrid An Fara Zawarcin Houssem

Dan wasan Real Madrid Gareth Bale

Dan wasa Gareth Bale zai cigaba da zama har na kimanin shekaru biyu a kungiyar Real Madrid, a cewar wakilinsa, domin kuwa tattaunawar komawarsa kungiyar Welshman bata yuwuba.

Duk da cewa ana ta rade radin cewar dan wasan mai shekaru 30 zai bar kungiyar, amma babu tabbacin hakan.

Kungiyar Juventus ta jera sahu da Manchester City wajen zawarcin dan wasan tsakiya na kungiyar Lyon Houssem Aouar. Dan wasan mai shekaru 21 akwai alamun zai bada mamaki a duniyar kwallon kasashen Turai.