Gasar AMVCA Ta Bana Ta Kayatar - Inji Kamal S. Alkali

Kamal S Alkali

A makon da ya gabata ne muka zanta da Kamal S Alkali furodusa a masana’antar Kannywood, wanda ya zaiyyana mana yadda gasar (AMVCA) Africa movie Viewer’s choice award, da aka gudanar karo na biyar a Jihar Legas.

Kamal Alkali, ya ce ana shiga gasar ne ta hanyar cika form a yanar gizo-gizo bayan an tallatawa ‘yan fim na daukacin Nahiyar Africa. Ya kara da cewa bai taba ganin gasa mai wahalar shiga kamar wannan ba musamman duba da irin girma da kuma sarkakiyar da wannan gasa.

Ku Duba Wannan Ma Mahesh Bhatt: Ya Kamata Dan Adam Ya Fahimci Banbancisa Da Dabba

Ya ce bayan jarumi yabi dukkan ka’idojin da aka gindaya na shiga gasar ne kana zai samu shiga, ya kuma kara da cewa gasar tana cikin Award wato kyaututtuka na biyar a duniya mussamam duba da yadda ake shirya gasar a a duniya.

Daga karshe Kamal, ya ce duk da bai samu damar cin kyautar ba, ya samu takardar yabo akan fim din sa.

Your browser doesn’t support HTML5

Gasar AMVCA Karo Na Biyar Ta Kayatar - Inji Furodusa Kamal