Malam Adnan Muktar Tudun Wada, shugaban hadakan kungiyoyin matasa a jihar Kano, ya bayyanar da irin yadda ake barin matasa baya a harkar gudanarwar gwamnatoci a matakai daban daban, da wanna suke ganin wannan wani koma bayane a bangaren demokaradiyya.
A matsayin su na matasa yakamata ace a basu kaso maitsoka wajen bada mukamai a gwamnati, kasancewar matsa suke da kaso mafi rinjaye a yawan mutanen Najeriya, don haka yakama a lura dasu matuka. Kuma yana ganin cewar su kansu matasa suna da nasu gudunwa da zasu bada a kowane mataki, musamman ma a wajen ciyar da kasa gaba, da wayar da kan al’uma, duk wannan wani hakkine da ya rataya a kan matasa.
Kuma matasa su sani cewar, sai sun tashi tsaye wajen neman ilimi da kuma kokarin amfani da wannan ilimin ta yadda yakamata. A karshe suna kara kira ga sababbin gwamnatoci da zasu shigo da su maida hankali wajen tallafawa matasa a bangarori daban daban, don hakika tallafawa matasa shine cigaban kasa baki daya.