Griezmann Ya Nuna Matukar Sha'awar Taka Leda Da Pogba

Kungiyar Barcelona zata tura wakilanta dan ganawa da masu ruwa da tsaki na kungiyar Atletico Madrid, domin kammala tattaunawa kan batun dawowar Antoine Griezmann.

Sai dai a gefe guda Griezmann, ya ce yana son yayi wasa da dan wasan tsakiya na Manchester united dan kasar Faransa Paul Pogba, amma haka ba wai shine yake nuni da cewar Griezmann, zai koma Manchester united da taka leda ba duk da cewar Manchester a baya ta nuna sha'awarta kan dan wasan.

Wata mujalla daga kasar jamus ta bayyana cewa tsohon Kocin kungiyar Borussia Dortmund, Thomas Tuchel, shine wanda zai maye gurbin Arsene Wenger, a kungiyar Arsenal da zarar ya bar aiki a kungiyar. Sai dai itama kungiyar Chelsea, tana bukatar ganin Kocin ya maye mata gurbin Antonio Conte.

Kocin kungiyar Liverpool, Jurgen Klopp ya nuna bukatar sa matuka da gaske kan sayen dan wasan gaba na RB Leipzig, mai suna Timo Werner, mai shekaru 22, da haihuwa inda yake da burin sa kudi fam miliyan £75 domin sayen dan wasan dan asalin kasar Jamus.

Shi kuwa dan wasan Liverpool na tsakiya Emre Can, mai shekaru 24 a duniya na shirin barin kungiyar ne a matsayin kyauta in har kungiyar bata kara masa albashinsa zuwa fan dubu £200 a duk sati ba.

Manchester City, da kungiyar Juventus suna kan kaiminsu na ganin sun dauke shi da zarar ya shirya barin kungiyar ta Liverpool.

Har ila yau Kungiyoyin biyu Juventus da Manchester City, sun sake jera sahu guda kan sayen dan wasan tsakiya na Arsenal Aaron Ramsey, wanda kwantirakin sa zai kare a karshen shekara mai zuwa a kungiyar Arsenal.

Manchester united, tana sha'awar ganin ta dauko dan wasan baya na Kungiyar Celtic, mai suna Kieran Tierney, Inter Milan ta sha gaban Manchester City da Barcelona kan daukar dan wasan baya na Lazio Stefan de Vrij, a matsayin kyauta a karshen kakar wasannin bana.

Your browser doesn’t support HTML5

Griezmann Ya Nuna Matukar Shi'awar Taka Leda Da Pogba