Gwamnatin Borno Zata Bayar Da Tukuicin Naira Miliyan 50 Ga Wanda Ya Taimaka Aka Samo Daliban Da Aka Sace

Wasu mutane kennan daga Gwoza, jihar Borno, da tashe-tashen hankula ya raba da gidajensu, suna taro a sansanin ‘yan gudun hijira a lokacin da gwamnan jihar Borno Kashim Shettima (babu hotonshi) a garin Mararaba Madagali, jihar Adamawa. Fabrairu 18, 2014.

Gwamnatin jihar Borno ta ce zata bayar da tukuicin Naira miliyan 50 ga duk wanda ya taimaka aka samo dalibai mata da aka sace su daga makarantar sakandaren garin Chibok.

Gwamna Kashim Shettima, shi ne ya bayyana wannan a ganawar da yayi yanzun nan da 'yan jarida a Maiduguri.

Yace 14 daga cikin wadannan dalibai sun samu damar kwacewa daga hannun wadanda suka sace su, kuma sun komo gidajensu.

A kasance da Dandalin VOA domin jin cikakken bayanin.