Gwanatin Nijar Ta Kafa Dokar Hana Safarar Jakkai Daga Kasar

Ganin yadda ake fitar da jakai masu tarin yawa a kowace rana daga cikin jamhuriyar Nijar, hukumomin kasar sun dauki matakin hana fitarwa ko safarar jakan zuwa kasashen da ake kai su domin fargaban barazanar karewar jakan a kasar ta Nijar baki daya.

Malam Abuba Malam Kaka, na ma’aikatar da ke kula da kiwon lafiyar dabbobi a birnin kwanni ya bayyana cewa wannan sabuwar doka an kafa ta ne saboda barazanar karewar su a kasar, ya kara da cewa yawan jakan da ake fitarwa a kowace rana karuwa suke. Ya ce kuma babbar matsalar ita ce masu sayen jakkan basa son wadanda suka tsufa, sai matasa ko masu ciki.

A kowace safiya masu safarar jakan ke kwararawa da su kasashe irin su Najeriya da Borkinafaso inda farashin su yayi tashin gwauron zabi, farashin jaki guda yakai kusan jaka dari na sefa, kwatankwacin Naira dubu sittin zuwa abin da yayi sama, maimakon naira dubu goma ko dubu ashirin a shekaraun da suka gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa akwai masu cin naman jakan a kasashen da ake kai su, lamarin dake matukar barazana ga rayuwar dabbobin.

Wannan mataki da hukumomin suka dauka yazo dai dai da lokacin da wata babbar mota makare da jakai tayi zo mu gama da wani tanki mai dauke da man fetur a hanyar fita daga Nijar zuwa kasar Borkina faso, lamarin da yayi sanadiyyar konewar jakai kusan dari biyu.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwanatin Nijar Ta Kafa Dokar Hana Safarar Jakkai Daga Kasar