WASHINGTON, DC —
Gwamnatin kasar Nijar, Kashe kimanin Saifa, miliya dubu 500,wajen sayen motocin ambulance 150 domin tallafawa fannin kiwon lafiya, a kasar, inda ake bukatar su.
Fatara da talauci da matsalar samarda sufirin marasa lafiya, na ci gaba da kasancewa tarnaki ga talakawan kasar ta Nijar.
Amma sai dai a cewar wasu daga cikin wadanda wakilin mu Abdoulaye Mamane Amadou yayi hira dasu, sun muna farin cikin da samu wanna tallafi na motocin Ambulance.
Suka ce samarda motocin zai taimaka wajen rege wasu wahalhalu da suke fuskanta kafin su isa da marasa lafiya zuwa Asibiti, musamman ma a karkara.
Your browser doesn’t support HTML5