Hada Hadar Kasuwanci Kan Yanar Gizo A Najeriya

Vietnam Google Challenger

A ci gaba da ake samu hada hadar kasuwanci kan shafukan yanar gizo a Najeriya da Afirka baki ‘daya, yanzu kamfanin Yudala ya kaddamar da shagonsa kan yanar gizo a Najeriya.

Baya ga haka kuma kamfanin ya kudiri aniyar ‘kara wasu shaguna na zahiri har hudu a jihar Lagos din Najeriya.

Yudala ya bayyana cewa yanzu haka ya fara sayar da kayayyaki daga manya manyan kamfanonuwan fasaha da aka sani wanda suka hada da: HP da Apple da Techno Mobile da InnJoo da Infinix, Dell, Cisco, Microsoft da dai sauran su.

Baya ga Yudala, wasu manya manyan kamfanonin fasaha su biyar sun kirkiro hanyar da zata rika taimakawa kananan ‘yan kasuwa wajen bunkasa harkar kasuwancin su a duniyar yanar gizo, inda duk mai son bude hanyar saye da sayarwa zai iya ziyartar shafin myshoppey.com.

Shafin myshoppey.com yana sayar da fili da taimakawa wajen gina shi akan yanar gizo, hakan zai taimakawa duk kanana da manyan ‘yan kasuwa da suke son bunkasa kasuwancin ta duniyar yanar gizo. ‘yan kasuwa zasu iya ziyartar wannan shafi domin ganin zabin da suke da shi, da fara bunkasa kasuwancin su kan yanar gizo.