Kungiyoyin kwallon kafa da dama a duniya sun maida hankalin su wajan saye da sayarwan ‘yan wasa, domin tinkarar kakar wasan bana 2017/18 a watan Agusta mai kamawa.
Sabon dan wasan da Manchester United ta saya daga kungiyar Everton Romelu Lukaku ya fara motsa jiki da kungiyar ta Manchester United a karon farko.
Chelsea tana daf da sayen dan wasan tsakiya na Monaco maisuna Bakayoko ita kuwa Tottenham tashi sahun zawarcin dan wasan gaba na Manchester City Kelechi Iheanacho.
Burnley tana neman mai tsaron baya na Sunderland maisuna Kone Lamine dan shekaru 28. Jose Mourinho ya bukaci kungiyarsa ta Manchester da ta biya fam miliyan £60 don ganin ta sayo masa dan wasan tsakiya na Tottenham Eric Dier.
Shi kuwa Arsene Wenger na Arsenal yace yana da karfin guiwar dan wasan tsakiyarsa, Alex Chamberlin na nan daram a kungiyar duk da yana da sauran watanni 12 kafin ya karkare kwantirakinsa a kungiyar.
Manchester City tana cikin jerin kungiyoyi hudu wanda suke kan gaba wajan ganin sun sayi mai tsaron baya na Real Sociedad Inigo Martinez akan kudi fam miliyan £27.
Chelsea tana shirin sayen dan wasan gaba daga Real Madrid maisuna Alvaro Morata akan zunzurutun kudi fam miliyan £70.