Hada Ruwa da Wutar Ultrasound Zai Iya Kankare Dauda - Inji wasu masu nazari

Yayinda ruwan pampo mai sanyi ka iya wanke wata daudar, ba za a iya cewa yana wanke duka ba. Amma da wasu manazarta su biyu a jami’ar Southampton suka dan kara hasken wutar ultrasound da ruwan, ya sami karfin fidda kwayoyin dauda daga sako-sako da lunguna. A cewar wakilin muryar Amurka Gearge Putic

Za a iya ganin barbashi ko digon maiko a kan hannun mutum a karkashin hasken wutar da ake kira ultraviolet a turance, amma wanke shi da ruwan sanyi abu ne mai wuya.

Jona kafar ruwa da hasken wutar ta Uultrasound ya sa ruwan ya sami karfin kankare datti cikin sauri, kuma ba tare da kawo wata illa ba yakan wanke fatar mutum ta fita kal.

Shirin mai suna Starsteam, wanda wasu masu nazari su biyu daga jami'ar Southampton, ta kasar Ingila suka kirkiro, ya dauki alwashin canza yadda mutane ke wanke jikinsu da kuma wasu kayayyakin da suke amfani da su, daga kayan kichin zuwa kayan aikin asibiti.