Hadin Gwiwa Da Wasu Gidajen Talabijin Domin Kaucewa Masu Satar Fasaha

Aminu Bala Mailalle

A shirinmu na nishadi a yau mun sami bakwanci jarumi, Aminu Bala Mailalle, mai bada umarni wanda ya fara harkar fim tun 1998.

Aminu Bala ya ce sha’awace ta ja shi ga harkar fim inda suka fara ba da niyyar samun kudi ba amma a yanzu harka ce mai bada kudi sosai.

Ya ce a yanzu ya fi sha’awar ya fito a bayan Fagge ba tare da masu kallo suna ganin sa ba.

Kawo yanzu dai yana bada umarnin a wani jerin wasan kwaikwayo wanda shi ne karo na farko kuma wasa ne na barkwanci.

Ko da ya ke ya ce wasan barkwancin ba zai fita kasuwa ba illa dai zasu yi hadin gwiwa da wasu gidajen talabijin domin su mayar da kudaden su domin kaucewa masu satar fasaha.

A fannin tsegumi kuwa jaruma Aisha Dan kano ta jaruma da ta jima a sahun furodoshi ta fara aikin wani fim din ta mai suna Kujerar Mata.