Alhamdulilah anyi zabe lafiya an kare lafiya, Allah yasa wadanda suka samu nasara su zama masu tausayin talakawa da aldalci a shugabancin su amen. Wasu matasa a jihar Kano, dake bayyana ra’ayinsu dangane da wannan zabe da aka gudanar, kuma suna ma wadannan shuwagabanin fatan alkhairi da jagorancin Allah.
Baya ga haka muna kara kira da wannan shuwagabanin da su dubi Allah, suyi aikin da yakamata don cigaban kasa da al’uma. Su kuma sani fa cewar lokaci yayi da yakama ta a dinga ba jama’a dammar fadin albarkacin bakinsu a harka yau da kullun na gudanar da mulki.
Kuma wadannan da aka zaba su maida hankali wajen cigaba da ayyukan a inda magaba tansu suka tsaya. Da fatar zasu bama harkar cigaba matukar mahimanci. A bangare daya kuma, al’umah su cigaba da yima wadannan shuwagabanni addu’a don neman jagoranci Allah, ba kawai mundinga yimusu Allah yawadarai ba, don duk addu’ar da mukayi ma shuwagabanninmu to it ace zata dinga binsu a koda yaushe.