Kafar sadarwa hanya ce mai sauki da mata masu kananan sana’oi zasu iya tallata kayayyakinsu a saukake, in ji Malama Maryam Haruna, wata masaniya a harkar kafar sadarwa ta zamani.
Ta bayyanawa wakiliyar DandalinVOA cewa kafar sadarwa hanya ce mafi sauke da mace zata tallata sana’ar ta har ta kai ta ga samun kasuwa ba tare da sun kai kudadensu gidajen radiyo ba domin a tallata musu hajja.
Ta ce cibiyarsu ta fasahar sadarwa da cigaban al’umma wato CITAD na koyawa mata masu kananan san’oi yadda zasu yi amfani da kafofin sadarwa domin amfana da cigaban da zamani yazo dashi.
Malama Maryam ta kara da cewa wani gudu ba hanzari ba ta ja hankalin mata da su nustu kafin amfani da kafofin sadarwa gudun kutse daga wasu bata gari da ke amfani da kafofin sadarwar.
Ta ce abu ne mai sauki , mace mai sana’a zata iya daukar hoton abinda take tallatawa ta sanya shi a kafar Facebook ko Instagram da dai sauransu tare da aderishen da za’a sami mutum domin sayan kayan.
Maryam ta ce kasashen da suka cigaba ta kafar sadarwa ake saye da sayarwa har kayayyaki su iske mutum ba tare da ya hadu da mai sayarwa ko mai saye ba.
Your browser doesn’t support HTML5