Hanyoyin Kariya Ga Cutar Amosanin Jini a Lokacin Hunturu

Kiwon lafia

Sanin kowane cewar lokacin sanyin hunturu lokaci ne na tashin tashinar cututuka, mafi akasari a kasashen Afrika. Don haka wannan lokaci ne da yakamata mutane su guji yin wasu ayyuka da kan zamo baraza ga lafiyar su.

Ta bakin wata baiwar Allah, wadda take fama da cetar Amosalin Jini wanda ake kira a turance Sickle. Ita dai wannan baiwar Allah, tayi karatunta na jami'a a bangaren ilimin kayoyin halitar da ke cikin jini da ba'a iya gani da idon.

Ta kuma yi wannan karatunne don tasan makamar aiki da kuma hanyar da zatabi don taimakama masu irin wadannan cutututukan. Ta kuma bayyana yadda take kula da kanta a wannan lokacin, wanda yake taimakamata don zama cikin koshin lafia. Ita dai wanna baiwar Allah tace idan mutane zasu kula da kansu kuma su kula da irin abincin da sukeci to zasu zauna lafia.

Ta kuma shawarci al’umah da suyi kokarin su kare iyalansu daga cutar cizon sauro da dai kokarin kwantar da kura don samun ingantaciyar lafia.

Your browser doesn’t support HTML5

Cutar Amosalin Jini