Hattara da Cuta Mai Hallaka Al'umah Baki Daya

Matasa

Mutuwar zuci tafi cutar sankaran jiki illa a rayuwa, mafi akasarin matasa da suka samu kansu cikin hali na mutuwar zuci, sukan kasance masu hadari ga rayuwar al’uma.

Idan kawai matasa suka me da kansu baya suna jiran ace gwamnati kadaice zata yimusu abu batare da sun tashi sun nema makansu wata hanya ba to, wannan shi ke kawo koma bayan cigaban kasa. Wani matashi Andy Bature yayi wannan kiran, ga 'yan uwanshi matasa.

Mafi akasari matasa da suka samu ilimin addini da na zamani sukan zamo masu hankali da kwazo fiye da wadanda basu da ko daya, dalili kuwa a nan shine duk wanda yake da ilimin addini to yakan zama mai bin koyarwar addininshi a kowane hali ya samu kanshi, kuma za’a ga cewar mu’amalarshi da ta saura ta banbanta. Kuma duk yadda ta kasance za’aganshi da wayewa wajen amfani da iliminshi na zamani.

Babban abu a nan shine matasa kada suyi dogaro da gwamnati su tashi tsaye wajen neman na kansu, wanda ta haka ne kawai zasu iya taimakama kasar su dama ita kanta gwanati.

A wannan zamani da a ke ciki yakamata ace a Najeriya matasa sun kai ga samar da wasu abubuwan more rayuwa na zamani, da yakamata ace wasu kasashe na zuwa kasar suna siya, ba kawai ace sai komai a siyo da ga wata kasa a kawo cikin kasar don amfani al’uma.