WASHINGTON, DC —
A shirinmu na nishadi a yau mun sami zantawa da Hauwa Abubakar wacce aka fi sani da Hauwa Waraka
Hauwa Waraka ta ce ta fara harkar fim shekaru goma da suka wuce inda ta ce fim din ta na Kona Gari na daga cikn fina-finai da suka fito da ita duniya ta santa.
Ta ce ta dauki harkar fim sana'a kuma tana da burin habaka shi ta kuma ce da zarar ta yi aure toh sai dai ta zama producer wato mai daukar nauyi yin fim.
A fanni tsegumi kuwa Fasihi mawaqi Hussaini Abubakar da aka fi sani da Hussainin Danko ya dawo daga Jamhuriyyar Nijar bisa wata gayyata da aka yi masa don gabatar da wasa a can kasar ta Nijar.