Hukumar dake kula da sha'anin wasannin kwallon kafa ta duniya FIFA, ta bayyana sunan shahararen dan wasan Gaba na kasar Portugal, mai taka leda a kungiyar kwallon kafa na Real Madrid, dake Kasar Spain, mai suna Cristiano, a matsayin gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya na shekara 2017 (World Best) bangaren maza.
Cristiano, ya haura kan abokin hamayyarsa Lionel Messi, na kasar Argentina, mai wasa a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona a kasar Spain.
Zaben ya wakanane jiya a birnin London, inda kaftin kaftin na kwallon kafa na kasashe da masu Horas da 'yan wasan kwallon kafa da kuma wasu zababbun 'yan jaridu marubuta labaran wasanni a duniya suka jefa kuri'un su wajan zaben gwarzon wannan shekarar, kamar yadda aka saba a duk shekara.
Cristiano Ronaldo, mai shekaru 32 da haihuwa ya sami kashi 43.16 a cikin dari sai takwararsa Lionel Messi, wanda ya sami maki 19.25 a matsayi na biyu.
Dan wasan PSG, dan kasar Brazil, Neymar, shi ya zamo na uku da kashi 6.97.
Ronaldo ya taimaka wa kungiyarsa ta Real Madrid, ta lashe kofin zakarun nahiyar Turai (UCL) a jere sau biyu, 2015/16 da 2016/17 inda a wasan karshe ya jefa kwallaye biyu a cikin kwallaye hudu da ta sha Juventus wanda aka tashi 4-1 hakan ya bata damar lashe kofin karo na goma sha biyu.
Haka kuma dan wasan ya taka rawar gani wajan wasanni 29 da ya buga a bangaren laliga na kasar Spain, 2016/17 inda ta jefa kwallaye 25 wanda haka ya wallafa wa kungiyar ta Real Madrid, lashe laliga 2016/17 bayan ta shafe shekaru biyar a Jere batare da ta dau kofin ba.
Wannan shine karo na biyar da Cristiano Ronaldo, ya lashe wannan kambun zakaran kwallon kafa na duniya, ya kuma lashe sau biyu a jere kenan. 2016/2017.
Bayan haka kuma An zabi Zinedine Zidane, mai horas da kungiyar Real Madrid ta kasar Spain, a matsayin Gwarzon Koci na shekara 2017, inda ya jagoranci kungiyar Real Madrid, ta lashe kofin zakarun nahiyar Turai UCL sau biyu a Jere 2015/16 da kuma 2016/17.
Your browser doesn’t support HTML5