A Kwai Bukatar Hukumar Yaki Da Cin Hanci Ta Sa Hannu Wajan Yaki Da Satar Jarabawa A Jamhuriyar Nijer

Lura da yadda satar jarabawa ta yi Kamari a ‘yan shekarun baya bayannan a jamhuriyar Nijar musamman a manyan birane inda ‘ya’yan manyan mutane da na attajirai ke amfani da gatanci domin cin jarabawar kammala karatu, yasa hukumomin ilimin boko a matakin sakandire suka gayyaci hukumar yaki da cin hanci da rashawa domin ta agaza wajan takama masu wannan mummunar dabi’a burki a cewar Malam Muhammadou Mai Daji, darakatan ma’aikatar jarabawa a ofishin ministan makarantun sakandire.

Malamin ya bayyana cewa tamkar yadda zaka je cikin kanti ka bada kudi ka sayi kaya, haka ake sayar da jarabawar, da zarar kana da kudin ka, sai kawai kaje ka biya ayi maka cuwa cuwa kamar yadda sauran miyagun jama’a suka dauki lokaci mai tsawo suna aikata irin wannan ayyukan ashsha.

Ya kara da cewa lallai yin haka bai kamanta a gaskiya, domin kudi jaka hamsin suke biya, haka wasu iyayen suke ba diyan su domin kawai su aikata irin wannan mugun aiki. Dan haka Idan gwamnati ta bari aka ci gaba da tabka wannan barna ai bai dace ba.

Ta dalilin haka ne aka fara neman hanyoyin da za’a yi yaki da wannan mummunar dabi’a, shugaban ya kara da cewa kusan shekaru uku Kenan da gwamnati ke ta kokarin bullo da hanyoyin da za’a magance wannan dabi’a ta sace sacen jarabawa.

Domin tabbatar da nasarar wannan shiri na hadin gwiwa hukumar yaki da karbar cin hanci da rashawa ta bayyana cewa ta dauki matakin aikawa da jami’an leken asiri a cibiyoyin jarabawa na jahohin kasar daban daban.

Saurari cikakken rahoton a nan.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Yaki Da Cin Hanci Ta Sa Hannu Wajan Yaki Da Satar Jarabawa A Jamhuriyar Nijer