A shirin mu na wasu fitattatun mata da suka taka wata muhimmiyar rawa a rayuwarsu a yau mun sami bakwancin wata matashiya yar shekaru 23 ga uku ya asalin jihar kano malama Azima Bashir.
Azima Bashir, dai ta ce ta yi karatun bokon ta ne duk a jihar kano, inda ta karancin aikin jarida a makarantar Aminu Kano legal studies da keke Kanon Najeriya, inda ta samu takardar diploma daga bisa ni ta tafi jami'ar Bayero ta Kano inda ta karanci har ila yau aikin jaridar amma a wannan karon sakamakon advance diploma wato takardar gaba da diploma a halin da ake ciki kuma Malama Azima na aikin jarida a wani gidan jarida a dai Kanon Najeriya.
Ta ce lokaci yayi da mata , matasa za su farka daga barcin da su ke yi dan su nemi ilimin boko a cewar ta shi ne gishirin zamana duniya mussamam ma a halin da ake ciki a yanzu da komai a ya'u yin sa cikin kwanciyar hankali sai da ilimi.
Ta kara da cewa yazama wajibi ga mata sun tashi tsaye wajan neman ilimi domin yana taimakawa gaya wajan tabiyar yara a wannan zamani.