A shirinmu na wasu muhimman mata da suka taka rawa a al’ummarsu a yau dandalin yayi baban kamu domin kuwa mun sami bakuncin wata fittaciyar lauya da ta ga jiya take ganin yau, a yau dai alewace amma irin ta da.
Fatima Ado Ahmad ta ce sunyi karatu amma irin ta da, inda a kansu ne aka daina aji bakwai a firamare, bayan kamala karatun sakandaren ta ne aka nema mata gurbin karatu tun tana ajin karshen, ta kuma sami damar karantar likitanci a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.
A shekarar farko saboda wasu dalilai da bata son bayyanawa aka dauko ta daga jam’iar Ahmadu Bello, bayan dawowarta ne ta nemi gurbin karatu a kwalejin kano wato Aminu Kano legal studies, ta karanci diploma bayan kamalla karatunta aka aurar da ita.
Ta kara da cewa sai akayi rashin sa’a gidan aurenta basa son karatun boko , sai surukanta suka nemi a kona takardun karatun ta amma hakarsu bata cimma ruwa ba, bayan shekaru uku sai aure ya mutu.
Fatima ta kara da cewa bayan fitowarta ne ta nemi aiki, ta kuma koma karatun digiri har ta kamala , sannan ta sake yin aure har ta kamalla ta kuma cigaba da wasu karatun na digiri na biyu har guda biyu.
Ta ce bayan wadannan karatun ba’a yi su ta sauki ba sai da aka fuskanci wasu gwagwarmayar karatu.
Toh fa ga hirar ta dauko dadi, mai sauraro ya yi dakun mu a mako mai zuwa domin jin ire-iren gwagwarmayar da aka fuskanta, a wajen karatu.
Your browser doesn’t support HTML5