Ina Sana'ar Komai da Ruwanka Zata Kaika

Matasa

Babu wata illa idan mutun yasa kanshi a cikin harkar sana’a kowace iri, amma abun dubawa a nan shine mutun yayi kokarin tsare gaskiya a kowane irin hali ya samu kanshi, musamman ma yanayin da ka iya zubar ma mutun da mutuncin sa.

Malam Habibu Bello Abubakar, wani matashi ne me sana’ar komai da ruwanka, musamman ma idan wannan sana’ar zata kawomishi abun da zaiyi lalurar shi batare da yaje wani guri yana karamar murya ba. Ya kasance yakanyi sana’o’I daban daban a kuma lokkutta da dama, kuma yakanyi kokarin ganin cewar wata sana’a bata hana wata ba a ko da yaushe.

Ya kan zama dillali na gidaje da ma sauran wasu harkoki, amma abu da yasa yayi karko a wadannan sana’o’in ba wani abu bane illa irin gaskiya da rikon amana da yasa a gaba, sune suka kai shi ga wannan mataki da yake yanzu.

Yayi kira ga matasa da su bada hima su tashi tsaye wajen neman na kansu batare da sun dogara ga wani ba ko kuma gwamnati, don tahaka ne kawai matasa zasu zama wasu abu a rayuwa nan gaba.