Inganta Ilimin Mata Na Bukatar Sa Hannun Al'umma

Hajiya Amina Hanga ce shugabar Gidauniyar Isa Wali, ƙungiyar da ke kula da tsaro, da harkokin mata da harkokin lafiya, kuma ta bayyana ilimin 'ya'ya mata a matsayin abu mai matuƙar muhimmanci ga al'uma, taƙara da cewa kashi biyu ne kawai daga cikin dari na mata ke samun kammala ilimin boko har ya zuwa matakin sakandire a arewacin ƙasar.

Wani binciken ƙididdigar lafiya na gundumomin ƙasa ya bayyana cewa kimanin kaso sittin daga cikin dari ne ake cirewa daga makarantun firamarare ko sakandire domin a aurar da su.

A cewar ta "mun mayar da hankali ne akan mata manya da yara akan inganta ilimi, da ilmin mata da lafiya musamman mata masu juna biyu, da kuma ƙwato mu su 'yancin su, rashin barin mata su kammala karatu yakan shafi rayuwar su baki daya musamman ganin yadda ake yawan sakin aure ko kuma rashin maji ko wani abu makamacin haka, sai kaga mata da yara ne ke shan wahala kwarai."

Ta kuma ci gaba da cewa "wannan yasa muke ta kokarin wayar da kan jama'a akan muhimmancin ilimin mata manya da ƙanana."

Daga karshe ta yi kira ga iyaye maza da mata da kuma hadin gwiwar al'uma, gwamnatoci kuma su tabbatar da daukar malamai kwararru domin ganin an inganta ilimin 'ya'ya mata.