Inter Milan Tace Ba Zata Sake Dan Wasan Ba

Jack Wilshere na Arsenal yace yana da yankinin samun kansa a cikin tawagar ‘yan wasan kasar Ingila karkashin maihoras da ita Southgate wanda zasu fafata a gasar cin kofin duniya 2018.

Shugaban kungiyar kwallon kafa na Inter Milan yace bazasu sake dan wasan su Joao Mario dan shekaru 24, a watan Janairu ba duk dacewar Manchester United da Paris Saint-Germain sun nuna sha'awar ganin sun dauke shi.

Liverpool tace bazata amince dan wasanta Daniel Sturridge ya bar kungiyar a watan Janairu ba dan wasan ya kwallafa ransa na ganin ya Koma wani kulob domin ya samu kansa na shega jerin sunayen ‘yan wasan kasar Ingila da zasu fafata a kofin duniya.

Westbromwich tace zata maida hankalinta wajan dauko dan wasan baya na Middleborough Ben Gibson, In har ta sayar da Jonny Evans.

Newcastle tana yunkurin ganin ta dauko dan wasan gaba ba Leicester City Islam Slimani mai shekaru 29, Napoli na zawarcin dan wasan baya na Manchester United Matteo Darmian dan shekaru 28, a watan Janairu, ita Manchester zagaye ta keyi don neman wani mai tsaron baya ba hago da zai maye gurbin sa.

Your browser doesn’t support HTML5

Inter Milan Tace Ba Zata Sake Dan Wasan Ba - 4:54"