Ita Kade ce Mace 'yar Majalisar Dattawa a duk Arewacin Najeriya

Daga cikin 'yan Majalisar dattawa dari da tara a wannan karon ma dai mata takwas ne kachal, a maimakon sa ran da mata sukayi cewa yawansu zai karu a majalisar, tunda yake mata takwas ne dama a cikin Majalisar dattawan da za'a rushe a kwanaki masu zuwa.

A Majalisar wakilai kuwa yanzu an samu ragin yawan mata da ka zaba daga ashirin da hudu zuwa goma sha shida al'amarin da daya daga cikin matan da wannan sabuwar guguwar ta hanata dawowa Majalisar Ka'amuna Ibrahim Khadi, tace reguwar mata bawai basu iya siyasa bane abun ya kasance siyasa ce ta kudi kuma mata basu da irin kudi da maza suke dashi.

Ita kuwa sabuwar zababbiyar 'yar Majalisar dattawa daga jihar Adamawa Binta Masi Garba, wace ta kasance ita kade ce mace 'yar Majalisar dattawa a duk arewacin Najeriya, cewa tayi ya kamata mata su suna samun kashi ashirin zuwa ashirin da biyar a Majalisa.